Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana ainihin dalilin aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

A ranar Litinin ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, lamarin da ya kawo karshen jita-jita da aka ta yi a kan sha’awarsa ta mukamin.

A jawabin nasa, ya ce dalilin da yasa ya fito takarar da kuma abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne karfafawa da kuma tabbatar da tsaron Najeriya da al’ummarta da kuma gyara tsarin shari’ar kasar ta fuskar kudadensu da sauran tsare-tsare na walwala da bin doka.

Osinbajo ya ci gaba da cewa, idan aka ba shi daman, zai haifar da juyin juya hali na noma wanda zai kara taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar tare da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa su bunkasa tare da samar da ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, tituna, layin dogo, manyan hanyoyin sadarwa, haɗin kai, da sauran gine-ginen ababen more rayuwa.

Mataimakin shugaban kasan ya kuma jajanta akan bukatar da ake da ita ta fannin tattalin arziki domin zai fito da wani yunkuri da zai sanya Najeriya a matsayin daya daga cikin sahun gaba wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin mutane.

Ya ce: “ Za’a tabbatar gwamnati, hukumominta, da masu kula da harkokinta sun yi wa ‘yan kasuwa hidima, samar da fasahar kere-kere da za ta samar da ayyukan yi ga miliyoyin jama’a, da inganta Shirye-shiryen Zuba Jari na Jama’a zuwa wani tsari mai cikakken tsari na jin dadin jama’a, tare da cika alkawarin dagawa ‘Yan Najeriya miliyan 100 su fita daga kangin talauci a cikin shekaru goma”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *