NDLEA ta kama fakiti 101 na hodar iblis a cikin barguna yara.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu buhunan hodar ibilis guda 101 da aka boye a cikin barguna yara a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, Ikeja, Legas.

Kakakin hukumar Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya bayyana ranar Lahadi, ya ce wani Akudirinwa Hilary Uchenna mai shekaru 52, wanda ya zo daga karamar hukumar Oru ta Gabas ta jihar Imo ne ya shigo da wannan haramtaccen maganin daga kasar Brazil.

Sanarwar ta ce, an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar 9 ga watan Afrilu a dakin taro na D-Arrival na filin jirgin sama na Legas a lokacin da ya dawo daga Sao Paulo Brazil ta Doha a cikin jirgin Qatar, yayin da fakiti 101 na magungunan class A mai nauyi sosai. An kwato kilogiram 13.2 daga cikin jakar na shi.

Babafemi ya ce yayin wata tattaunawa ta farko, Uchenna wanda ya yi ikirarin cewa shi kafinta ne ya amsa cewa za a biya shi Naira miliyan 5 kan safarar miyagun kwayoyi bayan ya yi nasarar kai kayan a Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *