Mutumn 2 sun mutu, 3 sun jikkata sakamakon ruftawar gini mai hawa daya a Hotoro.

Wasu almajirai 2 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 3 suma suka samu munanan raunuka sakamakon ruftawar wani bene mai hawa daya a unguwar Hotoro da ke bayan gidan mai na Chula a Kano.

Rahama Media ta ruwaito cewa wadanda suka rasu sun hada da Aliyu Sulaiman (mai shekaru 27) da kuma Abdulganiyyu Sulaiman daga kananan hukumomin Garko da Kibiya kamar yadda malaminsu Sulaiman Abubakar ya tabbatar.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:08 na safiyar ranar Asabar a lokacin da marigayiyar ke barci a karkashin ginin da ya rufta.

Ya ce ginin da bai kammala ba yana kusa da makarantar Al-Qur’ani ta gargajiya (Makarantar Allo) inda daliban da abin ya shafa ke zama na wucin gadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.