2023: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, saboda tsadar fom din takara inji wani dan takaran APC

Christopher Ojo, wani dan takarar dan majalisa a jam’iyyar APC, ya bayyana fushinsa akan tsadar farashin kudaden sayen fom din takara a gabanin zaben 2023. Yace matakin da jam’iyyun siyasa suka dauka shi ne yake tabbatar da cewa manyan kujerun siyasar kasar nan su ci gaba da rike madafun iko wanda hakan ya sabawa ma’anar “Not Too Young To Run Act

Yace: “Idan ba a fakaice ake ce mana mu jira wani lokaci ba ko watakila, mu shiga cikin ayyukan cin hanci da rashawa, a ina ne suke sa ran mu (matasa) za mu samu wannan makudan kudaden da za mu saya fom kawai.

“Daga abin da na gani ya zuwa yanzu, babu wata jam’iyya da ke sayar da fom kasa da Naira miliyan 3, an mance za a kashe makudan kudade wajen yakin neman zabe da sauran kayan aiki.
Ojo ya bukaci jam’iyyun siyasa da tuni suka kayyade farashin fom din da su sake duba tare da rage farashin”.

Ya yi nuni da cewa hakan ya hana matasa da dama tsayawa takara a zabe mai zuwa, shi yasa yake kira ga jam’iyyun siyasa suka kayyade farashin fom din da su sake duba tare da rage farashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *