Shugaba Biden ya gargadi China kan goyon bayan Rasha

Shugaba Biden na Amurka ya gargadi China kan irin abin da zai same ta muddin ta goyi bayan Rasha a yakin Ukraine, sai dai bai fito fili ya bayyana hukuncin ba.

Mista Biden ya furta hakan ne a lokacin da suka yi tattaunawa ta bidiyo ta kusan sa’a biyu da takwaran nasa na China, Xi Jinping, inda ganawar ta kasance ta farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine.

Manufar Shugaba Biden a wannan tattaunawa dai ita ce, ya san inda China ta karkata a wannan rikici.

Amurka ta fito fili ta nuna abin da take son Chinar ta yi, cewa ta kasance a bangaren da ya kasance daidai na tarihi, wato ta bi sahun masu sukar mamayar da Rasha ta yi wa makwabciyar tata, Ukraine.

Sai dai abin takaicin shi ne har zuwa yanzu Shugaba Xi Jinping ya yi tsayuwar gwaman jaki, a kan haka, inda ya ki ya soki Rasha ko ma amfani da kalmar mamaya a kan rikicin.

Wani babban jami’i ya ce Mista Biden ya fito fili karara a tattaunawar ya nuna abin da Amurka da kawayenta ke son China ta ayyana a kan wannan rikici, tare da gargadinta kan illar da za ta gamu da ita, idan har ta yi kokarin taimaka wa Rasha kauce wa jerin takunkumin da aka sanya mata, abin da Chinar ta musanta yi.

Amurka ba ta fito fili ta bayyana irin abin da zai samu Chinar ba, amma dai ana ganin ita ma za a nemi hukunta ta ne da takunkumin tattalin arziki, domin kasuwancinta da Amurka da kuma Tarayyar Turai ya kai na tiriliyoyin dala.

Ita ma China ta fitar da bayaninta na yadda ganawar shugabannin ta bidiyo ta kasance, inda ta ce ba wanda yake son wannan yaki, amma ba ta fito fili ta dora alhakin rigimar a kan Rasha ba ko kuma yin Allawadai da Shugaba Putin ba.

A halin da ake ciki kuma rahotanni sun ce mutum akalla 45 ne suka mutu a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wani barikin sojin Ukraine a birnin Mykolaiv, mai muhimmanci na kudancin kasar.

Masu aiko da rahotanni na kasashen Yamma, a yankin sun ce ‘yan Ukraine na ci gaba da kare birnin, inda dakarun Rasha suka yi tunga a wajen birnin, ta bangaren arewa maso gabas.

Birnin Mykolaiv, wanda ke da muhimmanci ga shirin Rasha na kama birni na uku mafi girma a Ukraine, Odessa, ya dage wajen tirje wa hare-haren sojin Rasha, a gabar tekun Bahar-Aswad, ko Bakin-Teku.

Birnin mai tashar jirgin ruwa ya sha ruwan bama-bamai daga Rasha tsawon makonni, bayan da aka kora dakarun Rashar baya, a lokacin da suka durfafo shi.

Shi kuwa a jawabin da ya saba gabatarwa ga al’ummar kasarsa da dare, Shugaba Zelenskiy na Ukraine ya nemi da su yi zaman tattaunawar zaman lafiya ta sosai da sosai da Rasha, yana mai gargadin cewa idan Rashar ta ci gaba da yakin to za ta dauki shekaru aru-aru kafin ta dawo yadda take

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *