‘Yan fashi sun sace mata da ƙananan yara a Zamfara tare da ƙona gidaje

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan fashin daji ne sun sace mata da ƙananan yara tare da ƙona gidaje da dama a garin Yar Katsina na Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun afka wa garin ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bungudu da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Laraba, inda suka harbi mutane da dama.

Sadik Abdullahi “Yar Katsina ya ce mutum ɗaya ya mutu sannan an kai uku asibiti sakamakon raunukan da suka ji daga harbe-harben.

Haka nan ‘yan bindigar sun tafi da mata da ƙananan yara kusan 15 bayan harin.

“Yanzu haka mutum kusan 3,000 sun tsere daga garin zuwa maƙota kamar garin Gusau da Wanke da Bungudu,” in ji Sadik.

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe ‘yan fashin dajin da take kira ‘yan ta’adda kusan 100 a yankin arewa maso yammacin ƙasar cikin mako biyu da suka gabata.

Sai dai duk da nasarar da jami’an tsaron ke cewa suna samu, har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da karkashe mazaiuna ƙauyuka kusan a kullum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *