Kotu ba ta da hurumin hana mu yin gyaran fuska ga dokar zaɓe’

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce za ta ci gaba da aikinta na gyaran fuska ga sabuwar dokar zabe ta 2022 duk da umarnin da wata kotu ta bayar wanda ya dakatar da hakan.

Babbar jam`iyyar hamayyar Najeriya ce wato PDP ta kai majalisar ƙara, inda ta ƙalubalanci aikin yi wa dokar gyara bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaɓa mata hannu.

Amma Majalisar Dattijan ta ce kotu ba ta da hurumin hana ‘yan majalisa ayyukansu na yau da kullum.

A yayin wata tattaunawa da BBC, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓe na majalisar ya shaida wa BBC cewa doka ta ce babu hurumin da za a shiga da za a hana su aikin da ya kamata a yi.

“Da mu Majalisar Dattijai da wakilai da ita kanta hukumar shari’a da kuma ɓangaren shugaban ƙasa, ɓangarori ne uku waɗanda suka riƙe gwamnati, akwai abubuwan da suke a cikin dokar mulkin Najeriya cewa ba za su hana mu yin aikin da muke yi ba na rana da rana ba, idan ba haka ba babu abin da zai iya yiwuwa a ƙasar.

“Za a iya cewa an yi kasafi sai wani alƙali ya ce kasafin nan bai yi daidai ba kada a yi aiki da shi, idan an bi wannan tsarin an tsayar da aikin shari’a,” in ji Sanata Gaya.

Ya ce dokar nan shugaban ƙasa ne ya kai musu ita kuma ra’ayinsa ce inda Sanatan ya ce za su duba su gani idan za su iya gyarawa su gyara idan kuma ba za su iya ba za su san abin da ya kamata su yi.

“Hurumin mu ne mu yi aikin da ya kamata mu yi ba sai an saka mana doka ba,” in ji Sanata Gaya

Sanata Gaya ya ce ba su da wata fargaba dangane da ko fushin kotu kan wannan batu inda ya ce “ba mu da wata damuwa, za mu yi baccinmu da ido biyu ma da yardar Allah, tun da ba mu yi laifin da kotu za ta ce a kamo mu ba,” in ji shi.

A watan Fabrairun 2022 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kai.

Sai dai bayan shugaban ya saka hannu kan dokar, daga baya ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu.

Sai dai daga baya Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarni ga majalisa ta dakatar da wannan gyaran fuska, bayan ƙarar da PDP ta shigar tana ƙalubalantar wannan mataki na neman sake yin wannan gyara kwanaki ƙalilan bayan shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sa wa dokar hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *