An fara shari’ar Abba Kyari da wasu mutum shida kan safarar hodar Ibilis

Babban jami’in dan sanda Abba Kyari da wasu mutum shida da ake tuhuma da safarar hodar ibilis sun isa wata babbar kotun da ke Abuja domin a fara shari’a kan laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ce ta shigar da karar ranar 28 ga watan Fabrairu tana tuhumarsa da safara da kuma yin cinikin hodar Iblis.

Jami’an tsaro dauke da makamai ne suka kai Abba Kyari da wadanda ake tuhumarsu da aikata laifin tare da shi kotun da misalin karfe 8:12 na saiyar yau cikin wata bakar motar bas samfurin Hiace.

Sauran mutanen da ake tuhumar su da aikata laifi tare da Abba Kyari sun hada da Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da Bawa James, mataimakin sufritandan ‘yan sanda da Simon Agirgba da kuma John Nuhu wadanda dukansu sufetan ‘yan sanda ne.

Sauran mutanen sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

Mutum biyu cikin wadanda ake tuhuma da mu’amalla da hodar Ibilis a shari’ar da aka gurfanar da Abba Kyari tare da wasu mutu shida sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Mutane biyun ba sa cikin ‘yan sanda hudun da ake tuhuma tare da babban jami’in ‘yan sandan.

Mutanen biyu wato Chibuna Umeibe da Emeka Ezenwanne sun ba lauyoyinsu mamaki bayan da suka amsa laigukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Sai dai Babban jami’in dan sanda Abba Kyari wanda hukumar NDLEA ke tuhuma da safarar hodar ibilis a wata shari’ar da ta gurfanar da shi a wata babbar kotun da ke Abuja ya musanta cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Hukumar hana tu’ammali da miyagu kwayoyi ta NDLEA ce ta gurfanar da Abba Kyari da wasu mutum shida a kotun.

Sauran mutanen da ake tuhumar su da aikata laifin tare da Abba Kyari sun hada da Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da Bawa James, mataimakin sufritandan ‘yan sanda da Simon Agirgba da kuma John Nuhu wadanda dukansu sufetan ‘yan sanda ne.

Sauran mutanen sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

Hukumar NDLEA ta ce Abba Kyari da wasu jami’an da ke tamaka masa sun yi awo gaba da kilo 21.25 na koken, hodar Iblis din da suka kwace a hannun wasu masu safarar ta, kuma hukumar ta ce abin da suka aikata laifi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *