Ƙarin ‘yan Najeriya daga Ukraine 709 sun koma gida cikin dare

Ƙarin ‘yan Najeriya 709 da suka maƙale sakamakon yaƙi a Ukraine sun sauka a Abuja a yau Lahadi daga Romania.

Matafiyan akasarinsu ɗalibai sun sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da misalin ƙarfe 12:30 na dare a jirgin Airpeace.

Wannan ne rukuni na uku da aka ɗebo daga ƙasashe maƙotan Ukraine da suka haɗa da Poland da Romania da Slovakia.

Hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta ce nan gaba kaɗan wani jirgin zai sauka a Abujar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *