Shugaban Ukraine ya sake jaddada manufar Ukraine ta shiga Tarayyar Turai

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya gaya wa majalisar dokokin Tarayyar Turai cewa kasarsa na kare ‘yanci, kuma ta lamunta da duk asarar da za ta yi a yakin da take yi da Rasha.

‘Yan majalisar sun tafa tare da jinjina masa sosai a lokacin da yake jawabin wanda aka gabatar ta bidiyo.

Mr Zelensky ya kafe cewa mutanensa ba za su karaya ba da mamayar ta Rasha, yana mai kira ga majalisa da ta bayar da dama Ukraine ta shiga Taryyar Turai.

Ya ce a je a zo a karshe, haske zai mamaye duhu, gaskiya za ta yi galaba a kan karya.

Tun da farko Shugaban na Ukraine ya zargi Rasha da aikata laifin yakita hanyar kaddamar da hare-haren makami masu linzami a tsakiyar birninKharkiv, inda suka kashe fararen hula dadama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *