Fargaba ta ƙaru a Ukraine bayan ganin ƙwambar motocin sojin Rasha mai tsawon kilomita 64

Fargaba na ƙaruwa a Ukraine a yayin da wata ƙwambar motocin sojin Rasha ta kutsa ƙasar.

Hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauka a ranar Litinin syn nuna wata ƙwambar motocin sojin Rasha mai tsawon kilomita 64 na tunkaarar shiga birnin Kyiv na Ukraine.

Wani kamfanin fasaha na Amurka Maxar ya ce hotunan sun nuna ɗaruruwan motocin soji masu sulke da tankokin yaƙi da sauran ababen hawa masu ɗauke da kayan amfani.

Rasha na ƙara ɗaukar matakan kusten soji bayan da ƴan Ukraine suka ce sun tafka asara sosai a kwanakin farko na yaƙin

Leave a Reply

Your email address will not be published.