Atiku ya kai wa Obasanjo ziyarar ban girma a gidansa

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa da ake Abeokuta.

“Na yi farin ciki da ganin tsohon maigidana, Cif Olusegun Obasanjo, a safiyar yau yayin wata ziyarar ban girma da na masa a gidansa na Abeokuta,” kamar yadda Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter tare da wallafa hotunansa tare da Obasanjo.

Ko da yake Atiku bai fito ya ayyana cewa zai tsaya takara ba a zaɓen 2023 amma ana ganin ziyarar ba ta rasa nasaba da manufarsa ta takarar shugaban ƙasa.

Bayan ganawa da Obasanjo, ya shaida wa manema labarai cewa ba da daɗewa zai ayyana takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Atiku ne ya yi wa Obasanjo mataimaki tsakanin 1999 zuwa 2007, kuma ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasa tun zaben 2007 da 2011 da 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *