Rasha ta ragargaza wuraren farar hula 33 cikin sa’o’i 24′

Ministan harkokin cikin gida na Ukraine ya bayyana cewa dakarun sojin Rasha na harin gwamman wuraren da farar hula suke a ƙasar.

“Rasha ta ce ba ta kai hari ga wuraren da farar hula suke zaune ba sai dai an kai hari ga wuraren farar hula 33 cikin sa’o’i 24,” kamar yadda Vadym Denysenko ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Dakarun Rasha sun shiga Kyiv babban birnin Ukraine inda suka bi ta arewa da gabashi da kudancin ƙasar.

Hukumomi a Ukraine sun shaida cewa tuni dakarun Rasha suka shiga birnin, inda suke buƙatar ƴan ƙasar idan aka ce musu kule su ce cas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *