NDLEA ta nesanta jami’anta da badakalar hodar Iblis

Badaƙalar kama DCP Abba Kyari kan zargin hannu a safarar hodar Iblis ta ɗauki sabon salo a ranar Laraba bayan da hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasar ta musanta cewa akwai hannun jami’anta a lamarin.

A ranar Litinin ne dai, rundunar ƴan sandan ƙasar yayin da take sanar da kama Abba Kyarin, ta ce asalin mutanen da aka kama da hodar ta Iblis a Enugu, sun shiga ƙasar ne da taimakon jami’an hukumar ta NDLEA.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ranar Laraba ɗauke da sa-hannun kakakinta Femi Babafemi, hukumar ta ce ba ta da wani dalili na ɓoye duk wani da bincike ya biyo ta kansa a muna-munar ta hodar Iblis mai nauyin kilogram 25 wadda DCP Abba Kyari ya jagoranta.

NDLEA ta ce ta duƙufa wajen amfani da hujjoji wajen gudanar bincikenta kuma duk wani murɗe gaskiya ba zai sa ta yi rauni ba.

Babu ko shakka hukumar na mayar da martani ne ga wasu bayanai da ke ƙunshe a cikin sanarwar da rundunar ƴan sandar ƙasar ta fitar ranar Litinin tana sanar da kama DCP Kyari da wasu jami’anta huɗu tare da miƙa su ga hukumar.

Sanarwar ƴan sandan dai ta yi zargin cewa jami’an ƴan sandan sun yi aikin batar da sahun hodar iblis din ce da hadin bakin wasu jami’an hukumar ta NDLEA da ke filin jirgin sama Enugu.

Sanarwar ta kuma ce mutanen biyu da suka zo da hodar Ibilis ɗin daga Habasha, sun tabbatar da cewa suna irin wannan hulɗa da jami’an hukumar da ke filin jirgin Akanu Ibiam da ke Enugu tun bara; kuma ko a wannan karon da aka kama su, jami’an hukumar ne suka share musu hanya; kasancewar an turo musu hotonsu da sauran bayanansu kafin su sauka a Enugu.

Don haka rundunar ƴan sandan ta ƙalubanci hukumar da ita ma ta bayyana sunayensu kuma ta ɗauki matakin hukunta su.

To sai dai wannan sanarwar da hukumar NDLEA ɗin ta fitar ta musanta hannun duk wani jami’inta a cikin wannan badakalar tana mai kafa hujja da zantarwar da DCP Kyari ya yi da jami’inta wanda ya tona shi da kuma bayanan ɗaya daga cikin yara Kyarin ASP Bawa James ya bayar cewa wani mai kwarmata bayanai daga cikin masu safarar ƙwayoyin ne ya kira su ƴan sanda kai tsaye daga Brazil domin sanar da su cewa ana nan tafe da wannan hodar.

Ta ce a bayanin da ya bayar, ASP James Bawa ya ce wani mai suna IK ne ya kira shi daga Brazil ya ƙyanƙyasa masa cewa wasu mutane biyu za su zo Enugu ta jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines da hodar Iblis da zimmar idan aka kama su a ƙwace hodar a sayar a ba shi na shi kaso.

NDLEA ta kara da cewa hakan ya nuna ƙarara cewa akwai tawagar ta Abba Kyari na da daɗɗiyar alaƙa da gungun masu safarar ƙwayoyin da ke Brazil.

Hukumar dai ta ce ta fitar da wannan bayanin ne domin gyara wasu kura-kurai da ke cikin bayanan da aka bayar a baya amma dai ba za ta raga wa duk wanda aka samu da hannu a ciki ba.

Ko dai wane ne ke da laifi dai damuwar ‘yan kasar ita ce wanda za su ba amana tsakanin ɓangarorin jami’an tsaron ƙasar daban-daban ganin yadda ake ci gaba da bankaɗo ɓa-ta-gari daga cikin su nan da can.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *