Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Wata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba Kyari na cikin wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.