Korona ta kashe ƙarin mutum ɗaya a Najeriya, 158 sun kamu

Ƙarin mutum 158 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya ranar Litinin, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

Kazalika cutar ta halaka ƙarin mutum ɗaya.

Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 11, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

Anambra-82
Lagos-35
Akwa Ibom-13
Cross River-7
Kwara-6
FCT-5
Gombe-3
Kaduna-3
Bayelsa-2
Kano-1
Nasarawa-1
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,181 ne suka harbiu da cutar, sannan kuma ta kashe mutum 3,136.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *