An Cafke Masu Safarar Makamai Zuwa Najeriya Daga Nijar

Jami’an tsaro a yankin Dakwaro da ke Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke wasu masu fasakwaurin makamai zuwa Najeriya.

Dubun masu fasakwaurin sun uku ta cika ne a yayin da suke shirin safarar makaman nasu zuwa Najeriya.

An yi garkuwa da ’yan kasuwa da ba a san adadinsu ba hanyar Kano
Bayan wata 7, Buhari ya sake bude Twitter a Najeriya
Gwamnan Jihar Maradi, Shu’aibu Abubakar, ya ziyarci yankin na Dakwaro inda ya jinjina wa jami’an tsaron a game da kokarinsu wajen dakile shirin na su.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun jima da daukar matakan yaki da masu safarar makamai zuwa kasashe da ke makwabtaka da kasar.

A baya-bayan nan ma sai da gwamnatin kasar ta tsare wasu jami’anta da ake zargin suna da hannu a irin wannan kazamar harka ta safarar haramtattun makamai da miyagun kwayoyi.

Najeriya ta jima tana kokawa kan yadda ake shigo da makamai daga kasashen makwabtanta, wanda hakan ke jefa rayuwar dubban mutane cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *