Zanga-zangar nuna adawa da matakin nuna sheidar karbar allurar Covid a Faransa

Dubban  jama’a ne suka fito a wata zanga-zangar nuna adawa da tsarin nan da gwamnatin Faransa ta nace a kan sa da ya shafi batun nuna sheidar karbar allurar rigakafin cutar Covid 19 a jiya asabar.

Zanga-zangar da ta gudana a wurarre da daman a birnin Paris da wasu yankunan kasar daban ,ta baiwa mutane da dama damar bayyana bacin ran su,inda wasu daga  suka yi amfani da wannan dama don nuna bacin ran su biyo bayan kalaman Shugaban kasar Emmanuel Macron a baya da dau alkawalin saka kafar wanda daya da mutanen da suka kaucewa karbar allurar.

Tarurrukan na jiya na da nasaba da siyasa,kasancewar an hango  wasu yan siyasa a bainan jama’a,yayinda wasu suka aike da sakonni ta bidiyo na nuna goyan bayan ga wasu daga cikin yan takara a zaben kasar ta Faransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *