‘Yan wasan Senegal 3 sun harbu da corona gabanin karawarsu da Zimbabwe

Tawagar kwallon kafar Senegal na shirin doka wasanta na yau karkashin gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Kamaru ba tare da ‘yan wasanta Kalidou Koulibaly da mai tsaron ragarta Edouard Mendy ba, wadanda suka harbu da corona gabanin wasan farko.

Teranga Lions wadda ta kai wasan karshe a gasar da ta gabata a 2019 kafin shan kaye hannun Algeria a Masar, na shirin haduwa da Zimbabwe ne anjima da yamma karkashin rukuninsu na B.

Rashin mai tsaron raga Mendy da mai tsaron baya Koulibaly da kuma Famara Diedhiou wadanda yanzu haka ke killace babban kalubale ne ga Senegal wadda za ta kammala wasannin gasar ba tare da Ima’ila Sarr ba wanda kungiyarsa Watford ta hana shi damar wakiltar kasarsa.

Sai dai duk da wannan kalubale mai horar da tawagar ta Teranga Lions, Aliou Cisse wanda ya amsa cewa suna cike da kalubale ya ce zasu shiga wasan cike da kwarin gwiwa iya yin nasara kan Zimbabwe.

Senegal wadda ke matsayin lamba 1 fagen tamaula a Afrika bisa jadawalin FIFA, ta na cikin jerin tawagogin da ake yiwa hasashen iya lashe kofin na Afrika bayan subuce mata a 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *