‘Yan bindiga sun saki karin dailban makarantar Birnin Yawuri 30

‘Yan bindiga sun saki dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, kuma malami daya na makarantar, bayan shafe watanni shida suna yin garkuwa da su.

A ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021 da ta gabata, gungun ‘yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tare da sace dalibai da ma’aikata.

Kafin tafka ta’asar dai, sai da ‘yan bindiga suka fafata da jami’an tsaron da ke gadin makarantar a birnin na Yawuri, inda kuma suka kashe jami’in dan sanda 1.

Tun a waccan lokacin ne dai gwamnatin jihar Kebbi ta yi watsi da batun tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka nemi kudin fansa.

Watanni hudu bayan sace daliban ne kuma aka fara sako 30 daga cikinsu tare da malamai 3, said ai babu tabbacin ko sai da aka biya kudin fansar su.

A jiya Asabar ne kuma mai baiwa gwamnan jihar ta Kebbi Atiku Bagudu shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya tabbatar da sakin wasu karin dalibain 30.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *