Hukumar yaki da sha dama fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Edo a Najeriya ta kama wani Tsoho dan shekaru 76 da haifuwa da laifin safarar tabar wiwi yayin da aka kama wani da ake zargin jami’in tsaro ne na bogi mai suna Godwin Ilevbare wanda aka fi sani da Edwin Agbon da shigo da cakulet da biskit. daga Canada zuwa Najeriya don sayarwa.
A ranar Juma’ar, 7 ga watan Junairu, 2022, ne aka kama mutumin mai suna Godwin, wanda aka fi sani da tsohon soja, a unguwar Egor da ke yankin Oredo na jihar Edo, yayin da aka kama shi a lokacin da ya ke jigilar kaya da aka yi safarar su zuwa Najeriya ta hanyar wani kamfanin sakonni.
Ta bakin hukumonin wannan yanki,wannan ba shi ne karo na farko da ake capke manyan mutane dake gudanar da irin wannan aiki.