Shugaba Buhari, Gwamnoni, Ministoci sun yi ta’aziyyar Sheikh Ahmad Bamba

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ya aike sakon ta’aziyyarsa ga al’ummar Musulmi bisa mutuwar Shehin Malami, Dr Ahmad Muhammad Ibrahim.

Shugaba Buhari yace za’a rika tunawa da Dr Ahmad Muhammad Bamba bisa gudunmuwar da ya baiwa addinin Musulunci da Najeriya da kuma soyayyarsa ga karantar da al’umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana sakon Buhari a jawabin da ya saki ranar Juma’a.

Buhari yace: “Lallai labari ne mai ban takaici muka samu na rasuwar Dr Ahmad. Mutum ne mai riko da addini kuma ya sadaukar da rayuwarsa bisa ilmin addini. Muna aike sakon ta’aziyya kuma muna addu’a Allah ya jikansa.”

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya bayyana mutuwar Dr Ahmad Bamba a matsayin babban rashi ga al’ummar jihar.

Ganduje ya siffantashi a matsayin mai kwadaitar da zaman lafiya cikin al’umma.

Sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *