Allah ya karbi rayuwar Sheikh Ahmad Bamba

Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh dakta Ahmad Ibrahim Bamba rasuwa.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin Ahmad Muhammad Ahmad ne sanar da rasuwar mahaifin nasa a shafinsa na Facebook a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce za a yi Sallar jana’izar Shiekh dakta Ahmad Ibrahim ne a Masallacin Darul Hadith da ke Tudun Yola, da ke cikin birnin Kano da misalin karfe 1:30 na ranar yau Juma’a.

Marigayi Dr. Ahmad ya kasance malami a Sashin koyar da ilimin Larabci na jami’ar Bayero a Kano da ke Najeriya, kafin daga bisani ya yi murabus ya shiga aikin wa’azin Musulunci gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *