Manchester United ta sha kaye har gida a hannun Wolves

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi rashin nasara da kwallo 1 mai ban haushi a wasansu da Wolverhampton Wanderers karkashin gasar firimiyar Ingila.

Wasan dai ya gudana ne a gidan United wato Old Trafford, wanda ke matsayin nasara ta farko da Wolves ta yi a gidan Red Devils tun shekarar 1980.

Haka zalika nasarar ta bai wa Wolves damar dawowa makwabciyar United din a teburin firimiya da tazarar maki 3 yayinda ita kuma Manchester United a bangare guda ke da tazarar maki 22 tsakaninta jagora kuma abokiyar dabinta Manchester City.

Alkaluma sun nuna yadda Manchester United ke da wasa a hannu yayin karawar kuma ita tafi yawan kai farmaki sai dai kawai rashin sa’a da ta dabaibayeta a karawar ta yau.

Manchester United din dai yanzu ta koma ta 7 a teburi bayan doka wasanni 19 wanda ke nuna akwai namijin aiki a gareta matukar ta na fatan shiga sahun ‘yan hudun saman teburin gasar don samun gurbi a gasar zakarun Turai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *