Jam’iyyun siyasar Guinee zasu tunkarar gwamnatin Sojin kasar

A Kasar Guinea jam’iyyun siyasa 128  sun sanar da aniyarsu ta tunkarar Gwamnatin mulkin sojin kasar don matsa masu su fito da jadawalin mika Mulki hannun farar hula ba tare da jinkiri ba.

Matakin da yan siyasar kasar suka dau na zuwa kusan kwannaki hudu da Amurka ta sanar da cire kasar ta Guinee daga cikin kasashen kungiyar ta AGOA masu huldar kasuwanci da Amurka.

A farkon watan janairun shekarar 2022, majalisar soji mai rike da mulkin kasar ta baiwa tsohon shugaban kasar Alpha Conde damar ficewa har idan ya na bukata.

Tsofin jami’an gwamnatin kasar Guinee Conakry © Matthias Raynal / RFI

 Mai Magana da yawun jam’iyyun siyasan  Cellou Dalein Diallo ya shaidawa taron manema labarai daukan wannan mataki a Conakry.

Leave a Reply

Your email address will not be published.