Iran ta sha alwashin daukar fansar kisan Qassem Soleimani kan Trump

Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya sha alwashin daukar fansa kan tsohon shugaban Amurka Donald Trump game da kisan babban kwamandan askawaran sojin juyin juya halin kasar Qassem Soleimani a shekarar 2020.

Kalaman Ebrahim Raisi da ke zuwa lokacin da ake addu’o’in cika shekaru 2 na kisan da Amurka ta yiwa babban kwamandan akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman birnin Bagdad ranar 3 ga watan Janairun shekarar ta 2020, ya ce daukar fansa kan kisan Soleimani ya zama wajibi agaresu.

Ba kadai a Iran ba, dukkanin kawayen kasar da ke yankin gabas ta tsakiya sun gudanar da jimamin na cika shekaru biyu da kisan na Qassem Soleiman tare da takwaransa na Iraqi wanda ya gudana bisa umarnin Donald Trump shugaban Amurka na wancan lokaci.

A cewar shugaba Ebrahim Raisi matukar ba a yiwa Donald Trump hukunci kan kisan gillar da ya yiwa kwamandojin da direbobinsu da masu tsaron lafiyarsu ba ko shakka babu za su dauki fansa da kansu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Iran ke shan alwashin daukar fansar ba, inda ko a washeharin farmakin wanda ya akshe Soleimani da Abu Mahdi al-Muhandis sai da kasar ta farmakin sansanin sojin Amurka da ke Iraqi kafin daga bisani mako guda Tsakani ta kakkabo jirgin Fasinjan Ukraine dauke da mutane 176 ko da yak e Tehran ta sanar da matsakin a matsayin kuskure maimakon daukar fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.