Firaministan Sudan ya yi murabus

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus bayan sama da watanni biyu da aka yi masa juyin mulki, yayin da kuma sojoji suka yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da su.

Tun dai shekara ta 2019, Sudan ke fuskantar cikas a yunkurinta na koma kan turbar demokuradiya bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir.

Sai dai kasar ta sake rincabewa bayan Janar Abdel Fattah Al-Burhan ya jagoranci juyin mulki a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata tare da tsare Hamdok.

Kodayake sojojin su saki Hamdok a ranar 21 ga watan Nuwamba karkashin wata yarjejeiya wadda a cikinta ya amince ya shirya zaben shugaban kasa a tsakiyar shekara ta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.