Ambaliyar ruwa ta kori dubban mutane a Malaysia

Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu, yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya ta’azzara ambaliya a wasu jihohi bakwai na Malaysia, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar, al’amarin da ya yi sanadiyyar rayukan mutune 50 ya zuwa yanzu.

Hukumomin kasar dai sun ce,  wannan ambaliyar ruwa ta tilasta kwashe sama da mutane 125,000 daga tsakiyar watan Disamba zuwa yanzu.

Hukumar Kula da Bala’o’i ta kasar ta ce, ana sa ran za a ci gaba da fuskantar munanan bala’o’i saboda matsalar yanayi ta tsawon makonni.

Kasar da ke kudu maso gabashin Asiya ta fuskanci yanayi mai zafi a karshen shekarar da ta wuce, tare da ambaliya da ta tilastawa jama’a yin kaura.

Sai dai hukumomi sun yi mamakin kwanakin da aka dauka ana tafka ruwan sama, wanda ya fara sauka daga ranar 17 ga watan Disamban da ya wuce, lamarin da ya sanya koguna suka tumbatsa tare da haifar da ambaliya a birane.

Leave a Reply

Your email address will not be published.