Allah ya yi wa Bashir Tofa rasuwa

Tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a shekarar 1993, Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yansa ta sanar a sanyin safiyar wannan Litinin.

Kwanaki uku da suka gabata, an yi ta yada labaran karya a shafukan sada zumunta game da rauswarsa, amma daya daga cikin  ‘ya’yansa mata ta fito ta karya labarin a wancan lokaci.

Za a ci gaba da tuna Tofa da gudunmawar da yake bayarwa wajen bada shawarwari domin ci gaban Najeriya da kuma yadda za a magance matsalolin da siuka yi mata dabaibayi.

Tofa ya tsaya takarar shugaban kasa  karkashin jam’iyyar NRC , inda ya fafata da MKO Abiola na jam’iyyar SDP a zaben da masana suka bayyana a matsayin mafi inganci da aka gudanar a tarihin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *