Al-Shebab ta kashe mutane tare da kona gidajensu

Mutane shida sun rasa rayukansu, sannan gidaje da dama sun kune kurmus sakamakon wani hari da mayakan Al-Shebab suka kaddamar a yankin Lamu da ke gabar ruwa a kasar Kenya.

Kwamishinan Gunzumar Lamu, Irungu Macharia ya tabbatar da aukuwar harin da kuma asasrar rayukan da aka samu, yana mai cewa, a halin yanzu, jamai’an tsaro na farautar maharan.

Mayakan Al-Shebab dai sun sha kaddamar da faramaki cikin Kenya saboda yadda gwamnatin kasar ta aike da dakaru zuwa Somalia a shekarar 2011  karkashin kungiyar Tarayar Afrika da zummar ragargazar masu ikirarijn jihadi.

Yankin na Lamu da aka kai wa harin na yau, na kan iyakar Kenya da Somalia kuma yana daga cikin wuraren da masu yawon bud ke kai ziyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *