‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga 38 tare da kame miyagu kusan dubu a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta sanar da kashe ‘yan bindiga 38 a jihar, yayin da ta kame wasu mutane miyagun mutanen 999, wadanda ake zargin suna da hannu wajen aikata mugana laifuka akalla 600.

Sai dai a yayin namijin kokarin murkushe gungun masu aikata laifukan ‘yan sanda 5 sun rasa rayukansu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Katsina Sunusi Buba ne ya bayyana samun nasarorin, yayin karin bayani kan ayyukan da suka gudanar a cikin shekarar 2021 da ka yi bankwana da ita.

Dangane da daruruwan masu aikata laifukan da suka cafke kuwa, kwamishin ‘yan sandan ta hannun mai magana da yawunsa SP. Gambo Isah, y ace 874 daga cikin 999 da suka cafke din sun fuskantar shari’a a kotuna.

Katsina na daga cikin Jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa daga muhallansu, inda was uke gudun hijira a sassan jihar ta Katsina, a yayin da wasu kuma suka tsere zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

A baya bayan nan ne kuma, gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake yin kira ga al’ummar jihar tasa, da su tashi tsaye domin baiwa kansu kariya da kuma tunkarar barazanar ‘yan bindiga da ke cigaba da kisan jama’a, cin zarafi da kuma yin garkuwa da mutane babu kakkautawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *