Tattaunawar Putin da Biden ta mai da hankali kan tankiyar kasashen 2

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun tattauna tsawon kusan sa’a 1 ta wayar tarho akan zaman tankiyar da ke tsakanin Rasha da kasashen yammacin Turai dangane da rikicin ta da Ukraine.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya bukaci tattaunawar da Biden, inda kuma suka shafe akalla mintuna 50 su na tattaunawa, kuma karo na biyu kenan da shugabannin 2 suka yi magana a cikin kasa da makwanni 4, bayan ganawarsu ta bidiyon na’ura a ranar 7 ga watan Disamba domin kokarin warware takaddamar da ke kara ruruwa a kan iyakokin gabashin Turai.

Tattaunawar ta jiya Alhamis ta kafa wani matakin ginshikin ganawar keke da keke da shugabannin na Amurka da Rasha za su yi cikin watan Janairu a birnin Geneva, inda ake fatan cimma matsaya da kuma hakura da wasu sharudda masu tsanani da bangarorin biyu suka gindaya a baya.

Amurka da kawayenta na Turai na zargin Rasha da barazanar mamaye kasar Ukraine, ganin yadda Rashar ta girke sojojin ta kimanin dubu 100,000 a kusa da kan iyakar kasar wato yankin Crimea, yankin da shugaba Putin ya yiwa mamaya a shekarar 2014.

Sai dai Putin, ya bayyana girke sojojinsa da ya yi a kusa da iyakar Ukraine a matsayin kariya daga mamayar kasashen yammacin duniya, musamman kungiyar tsaro ta NATO, duk da cewa ba a kai ga yiwa Ukraine tayin zama mamba a cikin kawancen sojojin kungiyar ba.

A farkon wannan watan ne Rasha ta zayyana wasu bukatu da dama da suka hada da ba da tabbacin cewa kungiyar tsaro ta NATO ba za ta kara fadada sansanonin sojin Amurka a tsoffin yankunan Tarayyar Soviet ba, sharadin da Amurkan ta yi fatali da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *