Mai yiwuwa Mali ta shafe shekaru 5 kafin komawa mulkin farar hula

Gwamnatin Mali da sojoji ke jagoranta ta bayyana cewa, mai yiwuwa kasar ta dauki tsawon shekaru biyar nan gaba kafin komawa kan tsarin mulkin dimokaradiya.

Wannan na zuwa ne bayan masu ruwa da tsaki sun gudanar da wani taron kwanaki hudu wanda ya tattauna kan gyaran kasar.

Sojojin sun ce, wa’adin rikon kwarya na watanni shida zuwa shekaru biyar, zai taimaka musu wajen gudanar da sahihin zabe.

A watan Agustan shekarar 2020, sojoji a karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita suka hambarar da zababben shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita, bayan zanga-zangar da ya fuskanta tsawon makwanni saboda zargin sa da cin hanci da kuma gaza kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi.

Bayan fuskantar matsain lamba daga Faransa da makwafta ne kuma, Kanal Goita ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a watan Fabrairun shekarar 2022 bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.PUBLICITÉ

Leave a Reply

Your email address will not be published.