Sojojin Sudan sun rufe birnin Khartoum domin dakile zanga-zangar kin gwamnati

Jami’an tsaron Sudan sun bazama kan titunan birnin Khartoum cikin shirin kar ta kwana, tare da datse babban birnin kasar daga yankunan da ke kewaye dashi domin dakile zanga-zangar da dubban mutane ssuka shirya yi kan adawa da juyin mulkin sojojin kasar.

Wani karin mataki da gwamnatin sojin kasar ta Sudan ta dauka kuma shi ne na katse intanet ta wayar salula, a daidai lokacin da masu adawa da gwamnatin mulkin sojan ke shirin gudanar da sabuwar zanga zanga.

Kawo yanzu dai an shafe makwanni masu rajin kare Dimokaradiya na gudanar da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 25 ga watan Oktoba, duk kuwa da murkushe masu zanga-zangar da yayi sanadin mutuwar mutane akalla 48, kamar yadda kwamitin likitoci masu zaman kansu a kasar ta Sudan ya tabbatar.

Bayanai daga Khartoum sun ce sojoji da ‘yan sanda da jami’an tsaro na yin sintiri a titunan birnin Khartoum, yayin da jami’an tsaron suka amfani da kwantenonin jigilar kayayyaki wajen toshe gadojin da ke kan kogin Nilu da suka hade babban birnin kasar da yankunan kewayensa da kuma birnin Omdurman.

Ko a zanga-zangar karshen da aka yi a ranar 26 ga watan Disamba, sai aka toshe gadojin, domin katse hanzarin masu boren daga karawa dubun dubatar mutane suka fantsama kan tituna karfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.