Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada Jose Peseiro dan kasar Portugal a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles.
A ranar Laraba ne dai, hukumar ta NFF ta tabbatar da sabon nadin bayan taron zartaswar da ta gudanar.
Sai dai, a cewar hukumar kwallon Najeriyar, Kocin Rikon Kwarya Augustine Eguavoen ne zai jagoranci ‘yan wasan kassar na Super Eagles zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka ta AFCON da za a fara a Kamaru, yayin da shi kuma sabon kocin tawagar na dindindin Mista Peseiro zai yi musu rakiya ne kawai, domin sa ido kan yadda lamurra za su gudana.
Da zarar kuma an kamala gasar ta AFCON zai fara aiki gadan gadan a matsayin babban kocin ‘yan wasan Najeriya.

Daga cikin fitattun ayyukan sabon kocin Najeriyar akwai zamansa mataimakin mai horas da kungiyar Real Madrid da ke gasar La Liga a shekarar 2003, inda yayi aiki tare da Carlos Queiroz, a karkashinsu ne kuma Madrid din ta lashe gasar La Liga, to amma daga bisani kungiyar ta sallame su, bayan gaza lashe kofin La Ligar a kakar wasa ta 2004 lokacub da Valencia ta yi nasarar lashe kofin.