Isra’ila ta karfafa wa Falasdinawa guiwa

Isra’ila ta gabatar da wani kunshin matakan karfafa gwiwa ga yankunan yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, bayan da Ministan Tsaron Kasar Benny Gantz ya karbi bakuncin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ziyararsa ta farko cikin shekaru da dama.

Abbas wanda ke jagorantar wata babbar tawaga a ziyararsa ta farko zuwa Isra’ila domin ganawa da mahukuntan kasar tun bayan shekara ta 2010, ya tattauna da Gantz a gidansa da ke tsakiyar garin Rosh HaAyin a cewar majiyoyi da kafafen yada labarai na Isra’ila.

A ranar Laraba, Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta ba da sanarwar matakan karfafa gwiwa ga gwamnatin Palasdinu.

Wadannan kuwa sun hada da Dala miliyan 32 daga cikin harajin da Isra’ila ta karba a madadin kasar, da kuma ba da izini ga karin ‘yan kasuwar Falasdinawa 600 da ke tsallakawa zuwa Isra’ila.

Har ila yau, ta sanar da hada kan wasu Falasdinawa 6,000 da ke zaune a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, wanda ke karkashin ikon Isra’ila tun yakin kwanaki shida na 1967.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *