INEC ta bukaci gaggauta kawo karshen rashin tsaro a sassan Najeriya

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, ta yi gargadin cewa zabukan shekara ta 2023, na iya zama cikin hatsari, matukar ba a kawo karshen  matsalar rashin tsaro a sassan kasar ba.

Yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja, kakakin hukumar zaben Festus Okoye, ya ce kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara da kuma rashin hukunta masu aikata laifuka matsaloli ne da ke kan gaba a tsakanin dalilan da za su iya hargitsa kyakkyawan yanayin da ake fatan samu na gudanar da zabukan na 2023.

INEC ta kuma kara da cewar tsoron da ma’aikatanta na wucin gadi ke yi kan tura su zuwa yankunan da ake fama da rikici matsala ce da ke ci mata tuwo a kwarya la’akari da cewar, akasarin ma’aikatan da ba na dindindin ba sama da miliyan daya, da suka yi aikin zaben shekarar 2019, sun nuna fargaba kan shiga aikin na 2023.

Sai dai hukumar zaben ta sha alwashin samar da mafita ga ma’aikanta kan yadda za su gudanar ayyukansu ba tare da fuskantar matsala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.