Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira da a kakaba wa gwamnatin Myanmar takunkumin hana shiga da makamai cikin kasar, tare da tsaurara takunkuman da ta kakaba mata biyo bayan kisan kiyashin da aka yi wa mutane sama da 30 a makon jiya.
Kisan dai ya faru ne yayin jajibirin ranar Kirsimeti a gabashin jihar Kayah, inda ‘yan tawaye masu rajin kare dimokradiyya ke fafatawa da sojoji, wadanda suka karbe mulki daga hannun gwamnatin farar hula a watan Fabrairu.
Babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar EU Josep Borrell ya ce mummunan ta’addancin da gwamnatin soji ta yi kan fararen hula da ma’aikatan jin kai, ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa don ladaftar da sojojin na Myanmar.
Kasashen yammacin Turai. dai sun dade da haramta cinikin makamai tsakaninsu da gwamnatin sojojin Myanmar, wadanda ko kafin juyin mulkin da suka yi, suke fuskantar zargin cin zarafin bil-Adama, saboda kisan kiyashin da suka rika yi wa ‘yan Kabilar Rohingya wadanda akasarinsu Musulmi ne.
A cikin watan Yuni Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’a don hana jigilar makamai zuwa Myanmar, amma kwamitinta na tsaro yaki amincewa da matakin, lamarin da ake dangantawa da alakar kasar ta Myanmar da kasashe masu kujerar dindindin, wato China da Rasha, wadanda su ne manyan masu samar da makamai gare ta.