Cutar Korona ta tilasta dage karawar Everton da Newcastle

An dage fafatwa tsakanin Everton da Newcastle a yau Alhamis saboda yadda ‘yan wasa ke fama da cutar Korona da kuma raunuka.


Newcastle ce ta gabatar da bukatar soke wasan, tana mai korafin cewa, da dama daga cikin ‘yan wasanta na fama da Korona da kuma raunuka.


Yanzu haka dai, kimanin wasanni 16 kenan aka dage a gasar firimiyar Ingila a cikin wannan wata na Disamba, yayin da kuma alkalumma suka tabbatar da cewar, fiye da mutane 100 da suka hada da ‘yan wasa da ma’aikatan kungiyoyin kwallon kafar da ke taka leda a gasar ta Firimiya ne suka kamu da cutar Korona a cikin watan Disamba.


Sai dai duk da karuwar masu Korona a tsakanin ‘yan wasa, kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya sun yi watsi da shawarar dakatar da kakar wasan da ake ciki zuwa wani lokaci a nan gaba, don dakile yaduwar cutar tsakanin ‘yan wasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *