Za mu daure duk wanda ya yi wa Ghana mummunan hasashe – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Ghana ta gargadi malaman addini da su kiyayi furta hasasshen aukuwar munanan al’amura a kasar, yayin da suke aikewa da sakwannin sabuwar shekara, idan kuma ba haka ba za su fuskanci hukuncin dauri na shekaru akalla biyar.

Jami’an tsaron sun ce, hasashen da wasu jagororin addini ke yi a Ghana, ya shafe shekaru da dama yana haifar da fargaba da kuma sanya rayukan ‘yan kasar cikin hatsari.

‘Yan sandan na Ghana ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta kara da cewar matakin sa ido kan jagororin addinin b aya nufin hukumomin tsaron Ghana suna adawa ne da bayyana hasashen aukuwar abubuwa a. kasar, illa kawai ba za su lamunci tayar da hankula ko kuma firgita jama’a ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *