Masu ruwa da tsaki kan tamaula sun bayyana damuwa dangane da rage yawan ‘yan kallon da gwamnatin Faransa ta yi a filayen wasanni da zummar dakile yaduwar annobar Korona, matakin da suka ce zai rage armashin wasannin da ya dawo tun bayan rashin walwalar da suka fuskanta a shekarar 2020, lokacin da annobar ta kai kololuwa.
A baya bayan nan ne dai Firaministan Faransa Jean Castex ya ce daga yanzu ‘yan kallo dubu 5 ne kawai ke da damar shiga filayen wasanni ciki har da na kwallon kafa domin baiwa idanunsu abinci kai tsaye, yayin da kuma adadin mutane dubu 2 za su rika shiga kallon wasannin da ake yi a rufaffun filaye.
Wannan doka dai za ta shafe makwanni uku tana aiki, daga ranar 3 ga watan Janairu.
A ranar Juma’a 7 ga watan na Janairu kuma za a cigaba da wasannin gasar Ligue 1, bayan da sabbin matakan takaita walwala da taron jama’a suka fara aiki, wadanda za su shafi wasannin da za a kara tsakanin Lyon da Paris Saint-Germain a ranar 9 ga wata, wasa mafi girma a a karshen mako, sai kuma karawa tsakanin Lille da Marseille.