Kotun Kamaru ta saki daliban da aka daure saboda barkwanci kan Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce an saki wasu dalibai uku ‘yan kasar Kamaru da aka yankewa hukuncin daurin shekaru goma-goma a gidan Yari bisa samunsu da yin barkwanci a kan kungiyar Boko Haram.

Wata kotun sojin kasar Kamaru ce dai ta samu Fomusoh Ivo Feh, da Afuh Nivelle Nfor, da kuma Azah Levis Gob da laifin rashin la’antar bayanan da ke da alaka da ta’addanci a watan Nuwamban shekarar 2016 bayan da suka yada wani sakon raha game da ‘yan Boko Haram a wayoyinsu.

Amnesty ta ce an sako daliban, wadanda ke tsare tun watan Janairun 2015 a karshen mako bayan da kotun kolin kasar ta Kamaru ta rage hukuncin daurin zuwa na shekaru biyar.

A cikin wata sanarwa da Amnesty ta fitar ta ce, daliban uku sun yi amfani ne da ‘yancin fadin albarkacin baki kawai, dan haka bai kamata a kama su ba tun da farko.

Kungiyar ta kara da cewa sakon da daliban suka yi musayarsa, yayi tsokaci ne kan wahalar samun aiki mai kyau ba tare da samun kwarewa sosai ba.PUBLICITÉ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *