Barcelona ta kulla yarjejeniya Ferran Torres

Kungiyar Barcelona ta ce a ranar Litinin mai zuwa 3 ga watan Janairu, za ta gabatar da Ferran Torres, sabon dan wasanta na gaba da ta saya daga Manchester City.

Torres dan kasar Spain ya kasance dan wasa mafi muhimmanci da Barcelona ta kulla yarjejeniya da shi, tun bayan rabuwa da gwarzonta Lionel Messi, wanda a yanzu yake taka leda a PSG da ke gasar League 1 a Faransa.

An dai cimma matsaya tsakanin City da Barcelona kan sauyin shekar Torres mai shekaru 21 akan euro miliyan 55, kudaden da wasu majiyoyi suka ce Barcelonan ta samu ne ta hanyar karbar bashi daga banki, la’akari da matsin tattalin arzkikin da take ciki.

Bayan komawarsa Manchester City daga Valencia, Ferran Torres ya ci kwallaye 16 daga cikin wasanni 43 da ya bugawa kungiyar ta City a ciki da wajen gasar Firimiya, inda ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofin gasar, da kuma kofin Carabao.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *