Ba zan sauya sheka daga PSG zuwa Madrid a Janairu ba – Mbappe

Kylian Mbappe ya yi alkawarin ba zai rabu da Paris Saint-Germain zuwa Real Madrid ba, a yayin hada-hadar kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu da ke shirin budewa.

A cewar Mbappe, har yanza yana nan daram a Faransa, zalika ya sha alwashin kammala kakar wasa ta bana a matsayin cikakken dan PSG, tare da taimaka mata wajen samun nasarori a wasannin da ta sanya a gaba.

Kalaman dan wasan na zuwa ne a yayin da ya rage watanni 6 yarjejeniyarsa ta kare da PSG, inda ake sa ran zai sauya sheka zuwa Real Madrid,  kungiyar da ya dade yana fatan komawa.

Kylian Mbappé REUTERS – BENOIT TESSIER

Tun a watan Agustan da ya gabata Madrid ta yi wa PSG tayin biyanta makudan kudaden kan matashin dan wasan na Faransa mai shekaru 23, amma Paris Saint Germain din ta yi fatali da tattaunawa kan cinikin.

A cikin watannin Fabarairu da Maris za a kara tsakanin PSG da Real Madrid a zagayen gasar cin kofin Zakarun Turai na biyu, kuma yayin tsokaci akan wasan, Mbappe ya ce ba shi da wani buri da ya wuce lallasa Madrid, kungiyar da ake sa ran zai koma nan da ‘yan watanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *