Sarkin Shaidanu ya mutu a Najeriya

Wani  boka a Najeriya da ake yi wa lakabi da Sarkin Shaidanu wanda kuma ke  da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 da mata 59, Simon Odo ya mutu.

Mista Odo wanda haifaffen garin Aji ne da ke Karamar Hukumar Igbo-Eze a jihar Enugu, ya mutu ne a sanyin safiyar jiya Talata bayan fama da gajeruwar jinya.

Daya daga cikin ‘ya’yansa, Emeka Odo ya tabbatar da mutuwar mahaifinsu ga Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, yana mai cewa mahaifin nasu ya mutu ne yana da shekaru 74.

Tuni aka fara shirye-shiryen yi masa jana’iza daidai da wasiyar da marigayin ya bar wa iyalansa, inda ya ce musu kar su kuskura su ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawarwaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *