An gudanar da jana’izar ‘dan majalisar Kaduna da ‘Yan bindiga suka kashe

Gwamnan Jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasiru El Rufai na daga cikin mutanen da suka halarci jana’izar ‘Dan Majalisar Dokokin jihar Rilwan Aminu Gadagau da ‘Yan bindiga suka yiwa kisan gilla a ranar litinin da ta gabata.

‘Yan bindigar sun hallaka ‘dan majalisar ne lokacin da suka afkawa matafiya akan hanyar Zaria zuwa Kaduna a yammacin litinin, abinda ya kaiga kashe mutane 3 da kuma kwashe wasu da dama inda suka kora su cikin daji.

El Rufai ya halarci jana’izar ce a Masallachin Juma’ar Tudun Wada tare da shugaban Majalisar Dokoki Yusuf Ibrahim Zailani da wasu ‘Yan majalisun jihar na da da na yanzu.

Kafin rasuwar sa Gadagau ya wakilci mazabar Giwa ta Yamma ne a majalisar dokokin Jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *