Takaddama mai zafi ta kaure tsakanin bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar da bangaren jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu dangane da zaben shugaban Najeriya lokacin da Atiku ya yiwa Jam’iyyar AC takara a shekarar 2007.
Wannan ya biyo bayan ikrarin tsohon gwamnan Osun Bisi Akande na cewar Atiku yaki fitar da kudin sa domin yakin neman zaben shugaban kasa lokacin da Jam’iyyar AC ta tsayar da shi takara, inda duk lokacin da aka bukaci kudin aiki sai ya ruga wurin Bola Tinubu.
Akande yace duk lokacin da jam’iyyar ta bukaci kudin da zata gudanar da aiki, sai Atiku ya cewa Bola Tinubu ya taimake su, abinda ke nuna cewar Tinubu ne kadai yake kashewa jam’iyyar kudi, bayan ya sadaukar da kudaden sa wajen gina sabuwar jam’iyyar ta AC a wancan lokaci wadda ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasar takara.
Sai dai kakakin Atikun Paul Ibe ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar wannan ba wani abin damuwa bane, domin kuwa a lokacin Tinubu da Atku suna inuwar jam’iyyar guda ne, saboda haka duk wanda ya baiwa jam’iyyar kudi ya bayar ne domin cimma muradun ta.
Ibe yace idan Atiku ya bukaci kudi daga Tinubu, ba yayi haka ne domin bukatar kan sa ba, sai dai bukatar jam’iyar ta su.
Allah yarufa asiri