Kakkarfar guguwar Tornadoes ta kashe mutane 94 a Amurka

Jami’an agaji na ci gaga da aikin ceto domin gano wadanda ke da sauran numfashi bayan da mahaukaciyar guguwa da aka yiwa lakabi da Tornadoes ta afkawa jihohi 6 tare da haddasa asarar rayukan akalla mutane 94 a kasar Amurka.

Joe Biden ya bayyana guguwar a matsayin daya daga cikin iftila’I mafi muni da aka taba gani a tarihin  kasar ta Amurka, inda tuni ya tura shugaba hukumar agajin gaggauwa na tarayya zuwa Kentucky domin jagorantar aikin tattara bayanai dangane da illolin da guguwar ta haddasa.

A jihar ta Kentucky kawai guguwar ta kasshe mutane 80 a cewar gwamna Andy Beshear, baya ga lalata dimbin gidaje da masana’antu musamman a garin Mayfield, yayin da guguwar ta kashe wasu mutanen 6 a Edwardsville da ke kudancin jihar Illinois.

Guguwar ta kashe wasu haddasa asarar rayukan mutane 4 a Tennesse,  mutane 2 Arkansar sannan ta hallaka wasu mutanen 2 a Missouri kafin isarta a jihar Mississipi, lamarin da ya sa ake fargabar cewar adadin wadanda suka rasa rayukansu zai iya zarta dari daya.PUBLICITÉ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *