Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF ta kori kocin Najeriya Gernot Rohr daga mukaminsa.
Hukumar ta NFF ta sanar da daukar matakin ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Lahadi, inda ta tabbatar da nadin Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwaryar tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles.
Eguavoen ya kasance mai horas da tawagar Super Eagles da ta kare kan matsayi na uku a gasar cin kofin Afrika da aka yi a kasar Masar cikin shekara ta 2006.
A halin yanzu Eguavoen zai jagoranci tawagar kwallon Najeriya har zuwa lokacin da za a nada mai horaswa na dindindin.