ECOWAS ta yi barazanar kara wa Mali takunkumai

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS sun sake jaddada bukatar su ta ganin shugabannin sojin Malin sun gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu ko kuma aka sanya musu sabbin takunkumin karya tattalin arziki a watan Janairu.

Bayan taron da shugabannin da suka gudanar a Najeriya, shugaban gudanarwar kungiyar Jean-Claude Brou yace shugabannin sun jaddada matsayin su na ganin an gudanar da zaben shugaban kasar Mali a ranar 27 ga watan Afrilu kamar yadda aka shirya a baya.

Shugaban sojin Mali Kanar Assimi Goita ya sanar da cewar a karshen watan Janairu mai zuwa zai shaidawa kungiyar ECOWAS shirin sa na gudanar da zabe mai zuwa.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed wajen taron ECOWAS © Nigeria presidency

Ita dai kungiyar ECOWAS ta dakatar da Mali daga cikin ta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi sau biyu a watan Agustan shekarar 2020 da watan Mayun shekarar 2021 tare da kakabawa shugabannin sojin haramcin tafiye tafiye da kuma rufe asusun ajiyar su.

Shugaban sojin Malin yace dalilin dage zaben watan Fabarairun ya biyo bayan taron kasa da ya kaddamar domin baiwa jama’a damar bayyana ra’ayoyin su akan yadda za’a samar da zaman lafiya a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *